ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyanawa takwaransa na Lebanon tausayawar abinda ya faru a kasar a jiya Talata, ya kuma kara da cewa; Iran, za ta kasance a tare da gwamnati da kuma al’ummar Lebanon.
Shugaban kasar Iran, Dr. Hassan Rauhani ne ya bayar da umranin a taimakawa al’ummar Lebanon wadanda su ka fuskanci hatsarin fashewar wasu sanadarori masu karfi da su ka haddasa asarar rayuka da ta dukiya.
Ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ta Lebanon ta bayyana cewa mutane da su ka kwanta dama, sun kai 100, yayin da wasu da su ka kai 4000 suka jikkata.
Har ila yau, ta fuskar asarar dukiya,tana tsakanin dala biliyan 3 zuwa biliyan 4.
342/